Labarai
Yadda bacci ya sace wasu barayi bayan kammala satar su a wani gida.
Wani abin al’ajabi ya auku a gidan wata tsohuwa da ke Hammanskraal a Pretoria cikin kasar Afirka ta kudu inda bacci ya kwashe wasu barayi biyu bayan sun gama tafka sata, LIB ta ruwaito.
Advertising
An samu bayanai akan yadda barayin suka balle kofar gidan matar a ranar Alhamis din da ta gabata, 14 ga watan Afirilu inda suka sace talabijin din bango, na’urar microwave, takalma da sauran abubuwa.
Sai dai yayin da suke kokarin fita gidan ne abin mamaki ya auku, don take anan bacci ya kwashe su.
Ga Bidiyon da hotunan barayin yadda sukai shame-shame suna bacci a kasa:
Advertising
Advertising