Yadda wata magaifiyar yara 8 ta dawo gida bayan shekara 20 da bacewar ta.
Wasu iyali sun tsunduma cikin farin ciki bayan mahaifiyarsu mai suna Florence Ikhine da ta bace a shekarar 2002 a garin Benin, jihar Edo shekaru 20 da suka gabata kwatsam sai gata ta bayyana. Ehima Elema wacce ta sanar da bacewan Florence a shekarar 2019 a shafin Facebook ita ta sake sanar da bayyanar ta.
Matar ta dawo ne bayan tsawon shekaru bata gida
EhimaTa ruwaito cewa matar mai shekaru 68 ta bayyana ne a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu,shekarar 2022 akan titin Ehaekpen, cikin garin Benin,inda daya daga cikin ‘ya’yanta ke zaune.
Legit.ng ta tattaro cewa ‘ya’yanta wadanda suka kasance yan mata da samari a lokacin da ta bace yanzu duk sun zama magidanta.
Iyalin matar sun tsunduma cikin farin ciki mara misaltuwa
Ehima ta sake faifan bidiyo da ke nuna irin yadda iyalan matar suka tsunduma cikin kaduwa da kuka saboda murnanr dawowar mahaifiyar su.
Inda ta wallafa cewa “ikon Allah baya karewa” ta rubuta: “Babu abinda ya gagari Allah. “Mahaifiyar abokina ta dawo gida bayan shekaru 20 da aka bayyana bacewar ta… “A cikin shekarar 2019 na yi wani rubutu na neman cigiyar neman mahaifiyar abokina… inda aka kwashe shekaru ana nemanta kafin daga baya aka gano ta.