Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Da haihuwar kilaki da Almajiri wanne yafi alkairi, Datti Assalafiy ya tofa albarkacin bakin sa

Da haihuwar kilaki da Almajiri wanne yafi alkairi, Datti Assalafiy ya tofa albarkacin bakin sa

Kamar yadda kuka sani Naziru Sarkin waka dai ya saki wani zazzafan martani akan ‘yan masana’antar kannywood, wanda ya karade kafafun sada zumun ta.

Advertising

To sai kuma shahararran marubucin nan Datti Assalafiy ya tofa albarkacin bakin sa kan lamarin inda yake cewa.

Naziru Sarkin Waka wanda asalinsa Almajiri ne ya saki zazzafan raddi ma wata gantalall!yar kila_ki ‘yar Hausa fim wacce a fakaice taci mutuncin Almajirai ma’abota Qur’ani.

Ga raddin da Naziru Sarkin Waka ya mata kamar haka:

Advertising

Ba al’amajirai bane ‘ya’yan da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana neman ‘ya’yan da iyayensu suka haifa kuma suka kasa kula da su to ka taho masana’antar fim!” ~Naziru Sarkin Waka.

Wannan raddin yayi daidai da abinda na fadi kwanaki, idan kana ganin cewa Datti Assalafiy ba dan fim bane, to ga Naziru nan a cikinsu yake, ya fimu sanin sirrinsu.

Wannan shine tsantar gaskiya, kuma ko ba komai da ka haifi yarinyar da zata shiga sana’ar karuwanc! ta dinga yawo da gantali ana
kwanc!ya da ita a manyan hotel na cikin gida da kasashen waje, to yafi ma alheri ka haifi Almajiri wanda zaiyi ta gantali domin ya koyi Qur’ani.

Mu a tsarin mu bama goyon baya bara, bara dabam yake da Almajiranci, to wakilan Yehodawa basa sukar bara kai tsaye, Almajiranci suke suka domin a hana karatun Qur’ani, ba zasuci nasara ba Insha Allah.

Allah Ka taimaki Qur’ani da Ma’abota Qur’ani.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button