Har yanzu ba’a daina yayin mu ba a kannywood ko a yanzu haka zamu iya dawowa, cewar tsohuwar jaruma Farida Jalal
Har yanzu ba'a daina yayin mu ba a kannywood ko a yanzu haka zamu iya dawowa, cewar tsohuwar jaruma Farida Jalal
Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood wacce tayi sharafin ta a shekarun baya wacce tayi kimanin shekaru 20 a masana’antar ana damawa da su “Farida Jalal.
A wata tattaunawa da suka yi da BBC Hausa a shirin su na daga bakin mai ita, ta bada tarihin rayuwar ta inda ta inda tace aan haife ta ne a garin Katsina inda a can tayi karatun ta.
A cikin shirar tasu ta bayyana cewa, ta dauki tsawon kimanin shekaru 20 a masana’antar kannywood, kuma har yanzu akwai fina-finan da take alfahari da su.
Inda ta fadi cewa, ko da aka daina ganin ta a shirin fina-finan masana’antar ba boyewa tayi ba ko da a yanzu aiki ya samu zasu fita kuma zasu yi.
Sai dai ta bayyana cewa, a yanayin harkar tasu wasu suna tasowa ne wasu kuma suna ficewa, don haka su sun tafi ne wasu kuma sun zo suna taka rawar gani.
Sai dai an yi mata tambaya kan cewa, a yanzu haka an daina yayin su ne, sai ta bada amsa da cewa.
A, a ba za a ce an dena yayinmu ba gaskiya. Kusan in ce dalilin kuwa shi ne, mun dade a masana’antar. To ko ba komai dai in dai za a yi zancen masana’antar Kannywood, to za a sako mu a ciki.
Ba za a ce an dena yayi ba. Har yanzu muna nan da masoyanmu, muna zumunci da su. Wasu ma har yanzu suna kallon irin gudunmawar da muka bayar a baya.
Ta ce yanzu ta fi karkata ne akan sana’ar saye da siyarwa sai kuma yabon ma’aiki wanda ake gayyatarsu biki, suna ko kuma maulidi.
Ta ce babban abinda ya janyo hankalinta har ta fara fim a masana’antar Kannywood shi ne yadda ta ga jarumai suna fadakarwa.
Dangane da aure kuwa ta ce ta taba yi amma yanzu ba ta da aure. Ta haifi yara biyu, sai dai daya ya mutu saura daya.