Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Wani furucin jaruma Rahama Sadau ya janyo mata cece-kuce kan cewa daga gida ake fara samin tarbiyya

Wani furucin jaruma Rahama Sadau ya janyo mata cece-kuce kan cewa daga gida ake fara samin tarbiyya

Kamar yadda kuka sani akwa jaruman masana’antar kannywood musamman mata wadan da suke wallafa bidiyo da hotunan su wanda basu dace ba shafukan sada zumun ta, domin ayi ta cece-kuce a kan su.

Advertising

Har ila yau jaruma Rahama Sadau tana daya daga cikin jaruman da duke janyowa masana’antar kannywood cece-kuce akan wasu halayen da take nunawa marasa kyau.

Wanda tayi fice wajan wallafa hotunan da basu dace ba har ma a yanzu abin nata ya zama ruwa dare, wanda a yanzu tayi wani furuci wanda ya sake haddasa wani cece-kucen.

Musamman masu bibiyar shafin Rahama Sadau na TikTok a ‘yan kwanakin nan zasu ga yadda take wallafa hotunan ta da shigar da bata dace ba.

Advertising

Kwatsam sai Jaruma Rahama Sadau ta yi wata wallafa a shafinta na Twitter wanda kana gani ka san neman magana ta ke yi, inda take cewa.

“Charity Begins At Home.”
Ma’ana Tarbiyya a gida take farawa.

Wannan karin maganar na bature ana amfaninda shi ne musamman idan an ga mutum yana yin wasu abubuwan da ba da dacewa.

Nan da nan mabiyanta suka fara caccakarta, tare da sukar iyayenta suna ganin ba a bata isashiyar tarbiyya ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa wanda Tashar “Tsakar gida” dake kan hamnajar Youtube ta wallafa, domin kuga abubuwan da Rahama Sadau aikata amma har wannan furucin yake fita daga bakin ta.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button