Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Fati Slow ta goyi bayan Naziru Sarkin waka ta maidawa da Nafisa Abdullahi zazzafan martani

Fati Slow ta goyi bayan Naziru Sarkin waka ta maidawa da Nafisa Abdullahi zazzafan martani

Kamar yadda kuka sani wata ‘yar hatsaniya ta barke tsakanin Narizu Sarkin Waka da jaruma Nafisa Abdullahi, tun bayan da tayi magana kan iyayan da duke haifar ‘yayan su amma basa iya kulawa da su.

Advertising

Inda har Nazirun ya maida martani ga ‘yan masana’antar kannywood tana mai cewa, ba Almajirai ne iyayan da suka haifa suka kasa kula da su ba idan kana neman ‘yayan da aka haifa aka kasa kula da su to kazo masana’antar kannywood.

Wannan magana ta Naziru Sarkin waka ta janyo cece-kuce inda ‘yan masana’antar kannywood din suka dunga maida masa da martani.

To a yanzu kuma tsohuwar jaruman masana’antar Fati Slow wacce a kwanakin baya Naziru Sarkin Waka ya bata kyautar Miliyan 1M, ta maidawa jaruma Nafisa Abdullahi martani inda take goyon bayan Naziru Sarkin Waka.

Advertising

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji martanin Fati Slow ga jaruma Nafisa Abdullahi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button