Advertising
Advertising
Uncategory

Yadda wani bam yay sanadiyar mutuwar mutun 1 ya kuma jirkata mutun 5 a jihar Yobe.

Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar a kalla mutum ɗaya, inda biyar kuma su ka raunata sakamakon tashin wani bam a jiya Lahadi a garin Gashua, Ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe.

Advertising

Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar, Dungus Abdulkarim ne ya faɗi hakan ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Litinin a Damaturu.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 zuwa 9:00 na dare a wani wajen sayar da abinci, inda ya ƙara da cewa harin an shirya shi ne takameme a kan wajen cin abincin.

“Ƙarar ta yi kama da ta bam.

Advertising

“Tuni a ka tura ƙwararrun jami’ai a kan Ababen fashewa su ka isa wajen domin tabbatar da abinda ya haddasa fashewar da kuma menene abin fashewar,” in ji Abdulkarim.

Ya ce waɗanda su ka ji rauni an kai su asibiti domin duba lafiyar su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button