Labaran Kannywood

Kada wanda ya sake kasa baki cikin wannan rigimar a barsu kawai suk kashe kansu cewar wata marubuciya.

Cikin Fushi da bacin rai fitacciyar Marubuciyar Adabin nan yar jihar Katsina,Hauwa’u Salisu Haupha, ta gargadi masu tsoma baki a kan rikicin da ya kaure tsakannin Nafisa Abdullahi da Naziru Sarkin waka,inda ta nemi jama’a su barsu su kashe kansu.

Haupha ta bayyana cewa “Da kai da ke da ku duk da ku nake!

Da kuke ta tada jijiyoyin wuya, kuna zagin wancan Nafisa,ko kuna zagin Naziru me ya shafe ku da su? Ku gaya min sun san da zamanku a duniyarmu? koko ɗiɗirin gwaɗa kiran miji da akaifa yasa kuka are zancensu da su ya shafa kuka yafa kuna ta soki burutsu?

Tsabar rashin aikin yi kun dage duk inda kuka ga Almajirai sai kun tsaya kun ɗauki hotunansu kun zo kuna wani damun mutane da maganar da ba ku ta shafa ba.

To ku sani ba amfani ga ɗaukar waɗannan hotuna, domin tamkar tozarci ne garesu! Haba jama’a abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin ƙwan makauniya? Su da suke cece kuce akwai wata a ƙasa tsakaninsu ku fa? Ko ko shiga shara ba shanu? Ya kamata mu san cewa azumi ake addini ya yi koyi da kowa ya yi abin da ya shafe shi ya bar abin da ba ruwansa”.

Marubuciyar ta kalubanci masu tado da maganar nan akan su saurara wa mutane “Don Allah ku saurara mana da zancen mutanen can su je su kashe kansu ma ba wani abu bane tunda duk sun balaga sun san hukuncin Allah”.

“Ni ƴan koren nan masu faɗin ra’ayinsu sun fi ban takaici domin su ke ƙarama wutar fetur ta ko’ina bayan ko sisi ba wanda zai baka garama su sun san nawa suka kwanta nawa suka samu har ta kai su ga hakan”.

Daga karshe Haupha ta Roki jama’a da su daina damun mutane da zancen Almajiran nan a koma wani shafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button