Advertising
Advertising
Labarai

Yadda hukumar kwana kwana ta ceto rayiwar wani zakara.

Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da ceto wani zakara mai shekara daya da ya fada rijiya a jihar.

Advertising

Kakakin Hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a unguwar Kwalli, cikin birnin Kano a yau Talata.

Ya ce hukumar, da misalin karfe 10:12 na safe ta samu kiran gaggawa be da ga wani mai suna Kamalu Garba, cewa an samu fadawa rijiya.

Kakakin ya kara da cewa a daidai karfe 10:15, sai jami’an hukumar su ka isa wajen da ha─Ćarin ya faru, inda su ka tarar cewa wani zakara ne ya fada cikin rijiya.

Advertising

Abdullahi ya ce tuni jami’an hukumar su ka ceto shekararren zakaran da ran sa, inda a cewar Kakakin, an kai shi sashin gaggawa na asibitin dabbobi na jihar domin kula wa da lafiyar sa.

Abdullahi ya ce tuni a ka sallami zakaran kuma ya dawo gida cikin koshin lafiya.Wasu mazauna unguwar dai sun ce zakaran ya fada rijiyar ne yayin da ya ke yin cara don burge wata kaza, ai kuwa, a cewar mazauna unguwar, bai aune ba sai jin shi ya yi a cikin rijiya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button