Naziru Sarkin Waka yayi amai ya lashe cikin wani Bidiyo da ya saki.
Bayan cece kuce da ake tsakanim jarumar masana’antar kannywood da fitacen mawaki sarkin waka nazir m Ahmad wanda kowa yane gani kamar da Nafisa Abdullahi take wanda ya sanya wasu suke ta maganganu da cewa saboda ta fita da cikin shirin sa ne na labarina.
Tashar tsakar gida ta fitar da sautin murya da sarkin waka Naziru M Ahmad yana chat da abokinsa inda yake gaya masa gaskiya cewa.
Sarkin waka tun fari shi ba da nafisa Abdullahi yake ba ya shiga twitter ne kawai yaga wasu yan masana’atar Kannywood suna dora hotunan alamajirai suna magana shiyasa yayi magana saboda abun yayi masa matuƙa zafi.
Yana chat na WhatsApp ne da wani abokinsa mai suna umar yace taya mutanenmu zasu kama dauko kwangilar yahudawa suna zuwa suna yadawa ai hakan bai dace ba.
Ga muryar tasa.