Advertising
Advertising
Labarai

Matashin daya auri budurwar data sami kunar wuta a fuskarta Allah ya albarkace su da haihuwa

Matashin daya auri budurwar data sami kunar wuta a fuskarta Allah ya albarkace su da haihuwa

Hakika wadannan bayin Allah sun burgeni matuka, musamman matashin da yayi jarunta ya auri matashiyar wacce fuskarta ta canza sakamakon kunar wuta, kamar yadda shafin Hausaloaded suka wallafa.

Advertising

Jama’a wannan shine soyayya na gaskiya, kyawun fuska ina daukarsa yaudara, domin kyan fuska wani abune kawai da yake gamsar da bukatar kwayar idanuwa.

Samari da ‘yan mata watakila ba zasu fahimci wannan zancen nawa ba a yanzu, amma duk wanda yayi aure ya haihu da matarsa haihuwa daya biyu zuwa uku zai fi kowa fahimtar abinda nake nufi fa cewa kyawun fuska yaudara ne kawai, bukatar ido yake gamsarwa.

Don Allah ‘yan uwa ku sama mana adireshi da nambar wayan wannan matashi, ya kamata muyi gangami mu tallafa musu da kudade suyi bukin suna.

Advertising

Muna rokon Allah Ya kara musu aminci da yalwar arziki a cikin aurensu, Allah Ya raya abinda suka samu, Ya sa su amfana duniya da lahira.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button