Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wani soja da aka kama yana da hannu wajen kungiyar ISWAP ya halaka kansa.

Wani sojan Najeriya wanda aka cafke bisa laifin haɗin guiwa da ‘yan ta’addan ISWAP, ya halaka kan sa yayin da ake tusa ƙeyar sa zuwa barikin sojoji. Jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Advertising

PRNigeria ta samu cewa sojan wanda yake tare da ɗaya daga cikin bataliyoyin sojin Najeriya da ke a yankin Arewa maso gabas, ɓangaren masu leƙen asiri ya gano cewa yana da hannu dumu-dumu a hare-haren kwana-kwanan nan da aka kai a wasu gidajen karuwai da mashaya barasa.

Yana da hannu a hare-haren da aka kai kwanan nan a garuruwan Geidam da Gashua cikin jihar Yobe

An cafke shi ne yayin da yake ƙoƙarin arcewa bayan ya fahimci cewa jami’an ɓangaren masu leƙen sirri gano duk wani motsin sa da yake yi da ‘yan ta’adda.

Advertising

Ya ƙwaci bindiga sannan ya halaka kan sa
Bayan an sanya masa ankwa, cikin hikima ya ƙwace bindiga daga wajen ɗaya daga masu rakiyar sa sannan ya halaka kan sa.

Haka kuma, ana cigaba da gudanar da bincike domin ganin an cafke sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a cikin sojojin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button