Labaran Kannywood

Gwanin ban sha’awa Bidiyon Jarumar Kannywood tare da ya’yan ta a kasa mai tsarki.

Daya daga cikin tsofaffin jarumai mata a masana’antar Kannywood kuma Amarya a halin yanzu Hafsat Idris itama tasamu damar zuwa aikin Ummarah na shekarar 2022 ita da ya’yan ta.

Jaruma Hafsat Idris wanda ta wallafa wasu hotuna da bidiyon ya’yan nata a kasa mai tsarki yayin dasuke aikin Ummarah wanda wannan shine karo na farko dataje aikin Ummarah da ya’yan nata.

Jarumar dai tanada ya’ya guda biyar hudu mata daya kuma namiji, inda a halin yanzu babbar yarta tayi aure a shekarar data gabata na 2021, saikuma sauran yan matan dasuke gabanta yanzu dakuma namiji guda daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button