Sarkin Musulmi ya bukaci mutane su fara neman wata tun daya yau.
Fadar sakin Musulmin Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll Ta bada sanar wa tun yanzu a fara neman saban watan Shawwal da zamu shiga Ranar Asabar.
Sanarwar ta fito daga ACR Zubairu Haruna Usman Wanda a yanzu haka shine shugaban gudanarwa a hukumar ta NSCIA, ya saka hannu A kwamitin ganin wata na kasa (NMSC).
Sarkin Ya bukaci al’ummah Musulmi da su fara neman wata tun daga ranar 30 ga watan Afrilu 2022, Dai dai da 29 watan Ramadan 1443.
A cikin sanarwar yace: “Idan Musulmai masu daraja suka ga jinjirin watan, Sarkin Musulmi zai sanar da ranar Lahadi 1 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal kuma ranar Idul Fitr ke nan. Amma, idan ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ta zama ranar Idul Fitr.
A karshe sanarwar ta ce Za’a iya tuntubar duka masu ruwa da tsakin ganin wata a duk fadin kasar nan wato (NMSC), Domin a sanar dasu inda aka ga watan dan tabbatar wa.