Labaran Kannywood

Sa’idu yayan Ado Gwanja yaki karbar tallafin Naira dubu hamsain 50K da Rarara yake rabawa ‘yan kannywood

Sa'idu yayan Ado Gwanja yaki karbar tallafin Naira dubu hamsain 50K da Rarara yake rabawa 'yan kannywood

Kamar yadda kuka sani a kwanakin nan ne Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya rabawa tsofaffin jaruman masana’antar kannywood kudi, wanda ba wannan ne farau ba domin a kwanakin baya ma ya musu irin wannan kyautar.

Sa’idu Isah Gwanja yaya ne ga mawaki Ado isa Gwanja kuma furodosa marketer ne kana shugaban gwanja global enterprise, wanda kuma a shekara 2007 ya kasance shugaban masu shirya finafinai na Kano.

Wanda zamu iya kira sa Uba kuma jigo masana’atar Kannywood domin ya bada gudunmawa matuka a fannin sa.

Kamar yadda Rarara ya saba a wannan Azumi ma ya ware sunayen jarumai da mawaka tsofaffi da matasa da zai bawa tallafin Azumi ciki kuma harda Sa’idu gwanja din.

Domin kamar yadda wasu ke duk da wayan can mukamai da sai’du ya rike a baya yanzu harkar ba kamar da ba musanman duba da irin yadda masana’antar ta juya akalarta daga harkat CD.

Wanda jaruma Aisha Humaira ce ta kira sunayen mutane hamsin uwaye mata da maza zasu amfana da shi.

Sai dai koda Sa’idu gwanja yaga sunansa a cikin jerin wadanda za’a baiwa tallafin dubu hamsin ransa ya baci da cewa, baya bukata zakuji bayyanin sa a cikin bidiyon da yayi wanda tashar tsakar gida na ruwaito.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button