Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Umma Sheru ta labarata Wani saban al’amari dake kokarin faruwa da Rukayya ta cikin labarina.

Fitacciyar jarumar Kannywood, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola na shirin raya sunnah

Advertising

kaman yadda kuka sani kwanakin baya Dasuka Gabata Jarumai da Dama A Masana’ntar sun shiga daga ciki, Ma’ana da yawansu sunyi Aure.

Jaruma Umma Shehu ce ta sanar da labarin shirye-shiryen auren abokiyar sana’ar tata
Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa wacce tauraronta ke kan haskawa, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola na shirin shiga daga ciki.

A cikin yan watannin nan ana ta shan shagalin bukukuwa a masana’antar ta kannywood, inda zuwa yanzu aka daura auren akalla jarumai hudu da furodusa daya.

Advertising

An fara ne da auren jarumai mata biyu a karshen watan Fabrairu wato Hafsat Idris Barauniya da Aisha Aliyu tsamiya, sai kuma na jaruma Hassana Moh’d wacce ta auri babban furodusan masana’antar, Abubakar Bashir Maishadda a ranar 13 ga watan Maris.

A yanzu kuma mun samu labarin shirye-shiryen auren Jaruma Teema Yola wanda abokiyar sana’arta, Umma Shehu ta sanar a shafinta na Instagram.

Koda dai Umma shehu bata bayyana ranar da za a daura auren Teema ba, ta tabbatar da cewar ita ce ta gaba a kan layi. Ta kuma wallafa bidiyon jarumar tare da wanda ke shirin zama angon nata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button