Labarai
Wata Sabuwa: Yadda aka sami gawar wata budirwa ta rataye kanta Sabida Auren dole.
A ranar Juma’a 29 ga watan Afirilun 2022 da misalin karfe 6.:00 na yamma ne dai labari ya cika unguwar cewar wata matar aure mai suna Sanayya Muhammad mai shekara 16 da a unguwar ta kashe kanta ta hanyar rataya.
Advertising
Bayanan da jaridar Aminiya ta samu shine andaura mata aure ne da angon nata mai suna Isa Jibrin mai shekara 35 wanda ta ce sam bata son shi.
Amaryar dai ’yar asalin garin Nasarawan Doya ce da ke Karamar Hukumar Makarfi da ke Jihar ta Kaduna.
Wani jami’in dan sanda wanda da shi ne aka je inda amaryar ta rataye kanta ya ce sun tarar da ita a mace.
Advertising
Kazalika, yace sun same ta a wani yanayi mara kyan gani, inda nan take suka dauki gawar suka kai ta asibiti domin fadada bincike.
Advertising