Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wata mata ta aike mijinta lahira bayan gano shi yana Soyayya da wata budirwa.

Wata mata ta na hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumi da laifin halaka mijinta bayan ya bayyana soyayyarsa ga wata matar, kamar yadda ‘yan sandan Texas na Amurka su ka bayyana hakan, LIB ta ruwaito.

Advertising

Yayin bayani a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, Harris County Sheriff, Ed Gonzalez ya bayyana yadda aka kama Carin Stewart mai shekary 51, wacce ta bayyana cewa da kanta ta halaka mijinta bayan sun yi hayaniya akan soyayyarsa da wata mata.

Yadda hukumar yan sanda taje ta sameshi da kuma irin mugan Raunikan da tayi masa

Yan sandan da aka tura gidan sun ga yadda ya raunana sakamakon harsasai wadanda matarsa ta harbe shi, bayan ya sanar da ita cewa yana soyayya da wata mata, a cewar Gonzalez kamar yada Fox News ta ruwaito.

Advertising

Gonzalez ya kara da cewa, take anan aka zarce da shi asabiti inda daga bisani ya mutu. An garkamr Stewart a gidan gyaran halin Harris County kuma an fara tuhumarta da kisan kai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button