ASUU: Za mu rufe filayen jirgin sama, tituna da wajen zaɓukan fidda-gwani-NANS
Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS ta yi barazanar rufe filayen jirgin sama, manyan tituna da guraren zaɓukan fidda-gwani a ƙasar nan domin nuna rashin jin daɗin ta da ƙarin tsawaita yajin aiki da ASUU ta yi na makonni 12.
Sanarwar da shigaban NANS na kasa ya fitar.
A wata sanarwa da Shugaban NANS na ƙasa, Sunday Asefon ya yi a jiya Litinin, ƙungiyar ta yi alla-wadai da abinda ta suffanta da halin ko-in-kula da gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke yi a kan lamarin.
Shugaban NANS ɗin ya kuma tabbatar da cewa ɗalibai za su yi tsinke a duk guraren zaɓukan fidda-gwani da taruka da jam’iyyu za su yi a ƙarshen watan Mayu.
Tun 12 ga watan Febrairu dai ASUU ta fara yajin aiki, inda lamarin ke ƙara ta’azzara, bayan da ta kasa cimma matsaya da gwamnatin taraiya.