Advertising
Advertising
Labarai

Sheikh Abduljabbar ya bukaci a barshi yay zaman sa a kotu ba tare da ya koma magarkama ba.

Malam Abduljabbar ya bukaci a barshi yay zamansa cikin kotu ba tare da an maidashi gidan mazaba.

Advertising

Hakan ya faru ne bayan da kotun ta ce lauyoyinsa sun miƙa mata takardar ficewa daga daga shari’ar.

Dai dai lokacin Malamanin yace kotu ta kyaleshi yayzamansa a kotun yaci gaba da kare kansa anan ne mai gabatar da ƙara ya tashi yace ai a ƙa’ida ba za’a ci gaba da shari’ar ba tare da Lauya ba.

A karshe dai kotu ta ce a rubuta a takarda zuwa ga Hukumar lauyoyi domin su bawa malam Sheikh Abduljabbar lauyoyi da zasu cigaba da kareshi.

Advertising

A yau Alhamis ne ake cigaba da gudanar da shari’ar Sheikh Abduljabbar da gwamnatin kano kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu ƙarƙashin jagorancin mai Sharia Ibrahim Sarki Yola.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button