Labarai
Wanni hanin ga Allah baiwa: Matar da aka kora daga gidan haya ta samu an gina mata wani a kano.
An Gina Mata Gida Kyauta Bayan An Kore Su Daga Gidan Haya A Kano Da Ita Da ‘Ya’yanta
Matar nan da Hotunan ta suka ringa yawo wanda ak koreta daga gidan hayar da suke ciki ita da ya yanta yanzu haka an gwangwaje ta da saban gida na zamani kuma kyauta.
Matar tasha wulakanci gurin mutanan da take haya sandiyar data sa ta zagaye wani fili da buhun sumunti suka ringa kwana a ciki.
Wani Bawan Allah ne mai suna Sani Rogo Aikawa ne ya jagoranci tallafawa matar. Inda aka gina mata gida ita da ‘ya’yanta a yankin Tokarawa unguwar Liman dake Kano.
Allah ya sakawa wanda ya dauki wannan nauyi d Alkhari Ameeen