Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yadda momee Gombe ta nuna rashin jin dadinta kan wasu kalamai da ake cewa ta fada.

A daren Jiya ne aka wayi gari da waɗansu zafafan hotuna na jarumar Kannywood, Momy Gombe inda aka yi amfani da wani shafin Twitter mai suna Momee Gombe aka ce ta bayyana cewa: “Samun Mace Irina sai namiji me sallar dare”, kalaman da su ka janyo cece-ku-ce matuƙa a shafin na tuwita da sauran shafukan zumunta.

Advertising

Sai dai a wani sautin murya da jarumar ta aiki Jaridar Arewa Media ta samu, ta bayyana cewa ba ta da masani akan wancan batu da aka ce ta ce, zuƙi ta mallace kawai da sunanta. Hasalima Jarumar ta bayyana cewa Instagram da Tik-Tok da su kaɗai ta ke amfani, saboda haka duk wani saƙo da za a ga da sunanta in ba a ɗaya daga cikin waɗannan shafuka ba ne to ba ita ba ce.

Daga ƙarshe jarumar ta yi fatan alkhairi ga masoyanta a duk inda su ke.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button