Labarai

Yadda wata budurwa ta maka mahaifin ta gaban kotu kan zargin ya hanata aure.

Matashiya mai suna Halima Yunusa a ranar Litinin dinnan ta maka mahaifinta a gaban wata kotun shari’a da ke Magajin Gari a jihar Kaduna bisa zargin kin bada aurenta ga masoyinta Bashir Yusuf.

Halima wacce ke zaune a garin Kasuwan Magani a karamar hukumar Chikun ta jihar kaduna ta shaidawa kotun cewa tana soyayya da Yusuf amma iyayenta sunki barinsu suyi Aure.

Mahaifin matashiyar, mai suna Ibrahim wanda yake sana’ar kasuwanci, ya shaida wa kotun cewa yana sane da irin tsananin soyayyar da ke tsakanin ‘yarsa da Yusuf.

Ya ce har yanzu Yusuf bai Cika sharudan aure da aka sani ba.

“Ya zo wurina ya nuna sha’awarsa Auren ‘yata. Na ce masa ya dawo tare da iyayensa da ’yan uwansa, Tun daga wannan rana Har zuwa yanzu bai dawo ba kusan shekara guda kenan.

Bayan shekara daya ya Sake dawo wa ya dauke ‘yata ya gudu da ita har na tsawon kwana uku, Daga baya muka ji sun dawo amma suna gidan ‘yar uwata.

Ya kara da cewa; Bamu tsaya bata lokaci ba muka sanar da ‘yan sanda inda akayi nasarar kama su tare da ladabtar da su,” in ji shi.

Bayan an sako su daga hannun ‘yan sanda, sai suka sake guduwa zuwa Abuja inda suka shafe makonni biyu.

A karshe dai na nemi ganawa da mahaifin yaron inda muka zauna muka tattauna sosai, mahaifin yaron ya nunamin cewar ba zai bar dansa ya auri ‘yata ba.

Daga karshe, mahaifin saurayin ya kai mu wurin hakimin kauyenmu inda aka tsara yarjejeniya da mu da shaidunmu muka sanya hannu kancewa ‘yata tafita harkar Dansu.

Halima ta shaidawa kotu cewar tana matukar son Yunusa, Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan ya saurari jawabin bangarori biyun, ya ce a shawarci mahaifin Yusuf da ya hakura ya bar yaran su yi aure.

“Idan ya ki, za mu yi musu aure a kotu ko da bai amince ba,” in ji shi.

Ya umurci mai karar da ta nemi gafarar iyayenta da ‘yan uwanta domin samun albarkarsu a rayuwarta.

Ya dage sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Mayu domin mahaifin Yusuf ya gurfana a gaban kotun domin yanke hukunci na karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button