Labarai

ABUN TAUSAYI: Mutumin da aka halakawa mata da yara hudu ya bayyana irin tashin hankalin daya shiga

Mutumin da aka kashe wa matarsa mai ciki wata tara da kuma ƴaƴa huɗu a jihar Anambra ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

Yace naji kamar an saka ni a cikin wuta saboda zafin da nake ji in ji Jibril Ahmed mijin matar da aka kashe da kuma ƴaƴansa huɗu.

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” kamar yadda ya shaidawa BBC

Ya ce a cikin satin nan matarsa za ta haihu amma aka kashe ta.

Ƴan sandan Najeriya sun ce sun kama ƴan bindigar da suka aikata kisan na mutum 12 da suka ƙunshi har da matar tasa mai ciki da ƴaƴanta huɗu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button