Labaran Kannywood
Adam a Zango Ya nuna farin ciki da godiya ga mai gidan sa Ali Nuhu bisa addu’ar da yay masa ta cika shekaru uku da Aure.
Akwana a tashi babu wani abu mai wahala wajen Allah, Adam A Zango da matarsa safeeya chalawa sun cika shekara uku da Aure.
Jarumi fitacce a masana’antar kannywood Adam A Zango sun cika shekaru uku da aure inda sukai ta wallafa hotunan su gwanin ban sha’awa.
Babban mai gida a wajen Adam A Zango Ali Nuhu ya taya yaran nasa murnar cika shekaru uku da aure ta hanyar yimusu fatan Alkhari gami da yimusu addu’a.
wannan itace wallfa jarumi a masana’antar kannywood wato Ali Nuhu Muhammad wadda yay wa babban yaran sa Adam A Zango da matarsa Safiya.