Turkashi: Yadda wata mata ta kama mijinta yana lalata da mahaifiyar sa.
Wata mata ‘yar shekara 23 ta ba da labarin ban mamaki a yanar gizo na Facebook.
Ta bukaci a kiyaye gaba daya.
A cewarta, kwanan nan ta shiga gidan su mijin ta ta tarar mijinata yana lalata tare da mahaifiyarsa Viralnow9ja ta ruwaito.
Ta bayyana yadda lamarin ya faru kaman haka, Ida take cewa:
Mijina ya ba ni mamakin da ban taba tunani ba a rayuwata kuma ina jin kamar in mutu. Ba zan iya ɗaukar wannan abun ba.
Mijina yana da shekara 25 ni kuma 23. Mun yi aure kusan shekara 2 yanzu, Kullum ina zuwa gidansu don gaida da mahaifiyarsa Mahaifin mijina ya mutu mahaifiyarsa kawai wadda yake tare da ita.
Na lura cewa mijina da mahaifiyarsa suna son juna sosai. Wani lokaci, idan na ziyarce shi, nakan gan shi yana kwance da kansa a kan cinyar mahaifiyarsa. Na kasance ina wasa da shi har ma na kira shi “Yaron mummy” sai ya yi dariya.
Kwanaki biyu da suka wuce. Na kai wa mijina ziyarar bazata abin da na gani ya jefa ni cikin tashin hankali. Na kasa yarda da abin da na gani idanuna.
Shigata gidan kai tsaye na nufi dakinsa tunda a nan ne muke haduwa. A nan ne na ga mijin nawa tsirara a kan gadonsa kuma a saman mahaifiyarsa. Yana lalata da ita.
Na kira sunansa da ihu na kusa na suma.
Su biyu su ka gigice da suka gan ni. Na gudu waje ina kuka kawai.
Tun daga nan mijina yake kirana yana aiko min da sakonnin waya game da yadda ake lalata da shi da sauran su. Amma ina cikin baƙin ciki sosai a yanzu. Ba na ma son tuna abun.