Labarai

Allahu Akbar: yadda wani tsoho Allah ya karbi rayiwar sa bayan gagowa daga sujjadah.

Wani bawan Allah Mai suna Ahmadu Idris Kanti Dan garin Rimaye ta karamar hukumar Ungogo ya rasu jim kadan bayan ya dago daga Sujjadar karshen Sallar Juma’a a cikin Masallacin Juma’a na Fagge.

Ana tsaka da jimami da tunanin yanda za ayi a gano Yan’uwan sa, sai Allah ya jeho wanda ya sanshi ya san Yan’uwan sa, inda nan da nan ya Kira Yan’uwan sa na jini ciki harda wani bawan Allah Mai suna Mahmuda Ibrahim Wanda yace marigayin kanin Mahaifiyar sa ne.

Mahmuda Ibrahim yace “Tun tasowar sa bai San adadin shekarun da Marigayi Ahmadu Kanti yayi yana zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Fagge ba.

Yace yanzu lokacin da zan fito kasuwa tare muka fito da shi, ya fito da mashin din sa ya taho Massallaci da shi. Tare muka fito da shi naga fitowarsa, da ya fito daga gida ba inda ya zarto sai nan Masallaci, da kansa yazo Masallacin Fagge”.

Tuni dai ‘Yan’uwan sa suka dauke shi domin zuwa yimasa Jana’iza Kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada bayan ‘Yan Sanda sun zo sun sheda lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button