Labaran Kannywood
Da Dumi Dumi: An tabbatar da dalilin Auren Aisha Humaira da Adam A Zango.
Ayaune wasu jerin hotunan Jarumi Adam a Zango tareda Jarumar Kannywood Aishatul Humaira suka fara yawo a kafafen sada zumunta.
Su dai wayannan hotuna na Adam a Zango da Aishatul Humaira, sun bayyana tamkar wasu sabbun ma’aurata Domin kuwa da kallonsu lokaci daya, Mutun zai iya cewa lokacin party din dinner dinsu ne sukaje.
Ganin wayannan hotuna yasa Jama’a girgiza matuka tareda shiga Cikin dunbin mamaki, inda daga Baya dayawa daga cikin Jama’a Suka Fara yanke hukuncin cewa Aishatul Humaira auren Jarumi Adam a Zango tayi.
Sai dai daga baya mun gano cewa wannan ba auren gaske bane, domin kuwa auren cikin wani Sabon film ne da suka fara dauka Mai suna “Rana Dubu”.