Asiri ya tonu Ashe Liilin Baba yanada wata matar kafin ya auri Ummi Rahab.
Da yawan mutane basu san da wannan labarin ba. cewa cewa Ummi Rahab itace matar Lilin Baba ta biyu, wato dai yanada wata matar kafın ya auri Ummi Rahab, wanda a gwari-gwari zamu iya cewa Ummi Rahab tanada kishiya, ko kuma abokiyar zama.
Yadda wannan alkawari ya samu cika
An daura auren fitaccen mawaki, Shu’aibu Ahmad Abbas wanda akafi sani da Lilin Baba, da fitacciyar jaruma Rahama Saleh Ahmad, wadda akafi sani da Ummi Rahab, Inda aka daura auren a ranar Asabar, 18 ga Yuni, wato a cikin wannan shekarar ta 2022.
Tuni Aka daura Auren nasu da misalin karfe 11:00 na safe a wani masallaci da ke NEPA Office, daura da gidan Bala Kasa, a unguwar Tudun Murtala dake jihar Kano, inda Lilin Baba ya biya sadakin Ummi Rahab N200,000 cif-cif.
Yadda jarumi Ali Nuhu ya taka rawa gani cikin wannan biki
Fitaccen jarumi Ali Nuhu shi ne waliyyin Lilin Baba, wanda ya karbi auren. Dama kuma shi ne wanda ya kai sadakin tun a watannin baya.
‘Yan fim sun yi wa abokan sana’ar tasu kara, domin kuwa kusan duk wani mai ji da kan sa a Kannywood da ya amsa sunan jarumi, furodusa, darakta, mawaki da sauran su ya halarci daurin auren.