Labaran Kannywood
Musa mai sana’a ya nemi yafiyar Hukuma Akan wasu kalamai da yayi a cikin fim dinsa.
Assalamualaikum Barkan mu da sake saduwa a wannan shafi namu mai albarka.
Advertising
Fitaccen Jarumi a masana’antar kannywood Musa Mai Sana’a Ya nemi yafiyar hukumar tace fina finai akan wani fim dinsa mai suna malamin Mata, Saka makon wani furici da yay.
Hukumar tace fina finai ta yiwa jarumin magana kan laifin, Inda jarumin nan danan ya nuna nadamar sa da kuma bawa hukumar hakuri akan wannan kalamai da aka fada a cikin fim din na sa.
Musa Mai Sana’a ya saki wani Bidiyo a shafin sa, Inda yake cewa babu wanda yafi karfin hukuma haka kuma babu wanda yafi karfin hukunci, Yana mai bawa hukumar hakuri ya kuma dau laifinsa kaman yadda zakuji a cikin Bidiyon.
Advertising
Advertising