Tofa haduwar Hannafi Ibro da Daddy Hikima Abale Ta bada citta
Jaruman wanda sun kasance matasane acikin masana’antar Kannywood domin kuwa shima Hannafi Rabilu Musa ibro yana matukar kokari acikin fina finan hausa, uwa uba kuma Abale daman shi kwararrene.
A karon farko dan Marigayi hannafi Rabilu Musa ibro da Daddy Hikima Abale sunfito a film daya masuna “Gidan Dambe” shirine wanda ya kunshi yadda ake damben gargajiya a kasar hausa.
Daddy Hikima Tsohon jarumi ne a Kannywood.
Abale dai yana daya daga cikin jarumai matasa dasuke da yawan masoya a arewacin najeriya tun lokacin daya fara taka rawa acikin Shirin “A DUNIYA” shiri mai dogon zango.
Haka zalika shima Hannafi Rabilu Musa ibro yana matukar kokari acikin fina finansa domin kuwa yakan kwatanta yadda mahaifinsa marigayi Rabilu Musa ibro yake kokarin nishadantar da masoyansa.
Sai dai wannan shirin maisuna “Gidan Dambe” haryanzu baifito kasuwa ba saidai mutane suna zaman jiran fitowar Shirin domin shirine wanda zai nishadantar da mutane matuka.