Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Turkashi An sake cire Ummi Alaga daga shirin Dadin kowa na tashar Arewa24.

A jiya kamfanin shirya Finafinai na Fkd Production suka dawo haska shirin su mai dogon Zango na Alaqa, A yau kuma aka dawo haska shirin Dadin kowa da gidan Tv Arewa24 ke haskawa duk Ranar Asabar.

Advertising

Duk wayannan shirye shirye ne da Jaruma Habiba Aliyu ke fitowa a ciki kuma take taka muhimmiyar rawa, A shirin dadin kowa tana fitowa a matsayin Yar Alkali Dikko kuma Budurwa Badaru yarinnya mai nutsuwa yar makaranta mai kamun kai yayin da a shirin Alaqa ta fito a matsayin ya ga wani Hamshagin mai kudi Alhaji Sale Alfundiqi.

Sai dai a watannin baya bayan dawowa daga hotun zango na farko na shirin Alaqa sai aka ga an maye gurbin Ummi da jaruma Maryam Yahaya wanda har hakan yaso ya zama abun magana inda yan kallo suka dinga korafin kasancewar ta taso da farin jini ta fara samun yan kallo mabiya.

Mun tattauna da Sarki Ali Nuhu a yayin da muka kai masa ziyara ofishin sa dake Nassarawa GRA inda ya tabbatar mana wani abu jarumar tayi da yasa ya cire ta daga shirin bawai dan yagi son Maryam ba ba kuma dan ita ba’a sonta ba sai dan kare martabar ta da kuma martabarsa da kamfanin sa dama masana’antar inda har ya bayyana cigaba da sata a film din ka iya zamar mata matsala wanda shi a shawarar sa ma da ta dan yi shiru ta rage fitowa a film har sai sun shagakkan disalar ko kuma tayi aure.

Advertising

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button