Labaran Kannywood

Badala a zahiri Video wasu maza da mata da suke tkar rawa a Gombe

Daga Abdullahi Yakubu

Wadannan wasu samari ne maza da mata galibin su ‘yan kimanin shekaru 13-19 kusan mutun 34 jami’an tsaro na hukumar Civil Defence reshen jihar Gombe suka kama su suna rawan batsa a wani gidan karuwai (Brethol), kashi 80% cikin wadannan matasa an kama su ne suna rawar tsirara ba kaya a jikin su.

Babban abun bakin cikin shine wasu da ake ganin manya ne ko masu fada aji a gari ana zargi cewa sune masu tallafawa da bada kariya ga wannan aikin ashararanci.

Tabbass idan ana aikata irin wadannan ayyuka kuma kowa yaja bakin shi yayi shiru hukuma kuma taki daukan mataki to fah abun da zai biyo baya ba zaiyiwa kowa dadi ba.

Ni kam shin a wace irin al’umma muke rayuwa ne kam!!!?

Allah ya sakawa Commandant na Nigeria Security and Civil Defence Corps reshen jihar Gombe, Allah ya kara masa taimako da kariya da sauran mataimakan sa na kwarai, Allah ya kiyaye mana zurri’ah, Allah yasa mu wanye lafiya.

Mungode da bibiyar shafin mu ku cigaba da kasancewa damu dan samun zafafan labarai.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button