Jaruma Hadiza Ali Gabon Ta musa alakar ta da Shuhu Musa Gabam Wani labari da gidan jarida suka wallafa.
Jaruma Hadiza Gabon ta musa kalaman da gidan jarida suka wallafa akan Shehu Jarumar Kannywood, Hajiya Hadiza Aliyu, wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa ta jini da sanannen ɗan siyasar nan na Jihar Bauchi kuma Shugaban jam’iyyar ‘Social Democratic Party’ (SDP) na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam.
Wata jarida Mai aikin ta a intanet mai suna ‘Grassroots Africa’ ta wallafa wani labari a gidan yanar ta cewa wai Hadiza Gabon ƙanwa ce shaƙiƙiya ga shi Shehu Gabam.
A rahoton da ta yaɗa mai taken “Actress Hadiza Gabam, a Nigerian, Sister to former Jonathan’s protocol” wato Jaruma Hadiza Gabam ‘yar Nijeriya ce kuma ƙanwar tsohon jami’in Jonathan’, jaridar ta bayyana cewa buga labarin da ta yi zai kawo ƙarshen tunanin da ake yi na cewar Hadiza ‘yar ƙasar Gabon ce.
“Ɗan jaridar wanda tsohon a harkar Sani Muhammad Sani ya rubuta da hannun sa, an ce: Abin da ya faru farko iyayen ta ba su amince mata ta shiga Sana’ar fim ba, wanda Dalilin hakan ne ya sa ta riƙa ɓoye gaskiyar Labarin inda ta fito kuma ba ta taɓa faɗa wa duniya gaskiyar yadda ake rubuta sunan ‘yan gidan su ba, wato Gabam.”
Wasu daga cikin aminan jarumar, irin su fitacciyar mawaƙiyar nan Sadiya Yarima, sun ƙaryata labarin tare da tabbatar da cewa Hadiza ‘yar asalin kasar Gabon ce.
Tsohon mai gidan ta a harkar fim fitaccen furodusan nan da ke Kaduna, Alhaji Yakubu Lere, ya ce mawallafin wancan labarin “bai san Hadiza Gabon ba kwata kwata.
Lere wanda shi ne ya shirya fim ɗin “Wasila” ya ce hasali ma dai Hadiza ta zo Nijeriya ne saboda ni. Kuma wani ya ce wai ‘yar Bauchi ce, bai ma san komai game da ita ba kenan,” inji shi.