Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Da wasu mutanen ke bada Aljanna da basu bawa yan film ba cewar jarumar Kannywood Hauwa Waraka.

Jaruma Hauwa Abubakar da aka fi sani da Hauwa waraka jaruma ce da tayi fice wajen fitowa a finafinai musamman na bariki ko fitowa a siffar karuwa ko yar’duniya wanda wanda wannan yasa har wasu kannyi mata wani kallo na daban a rayuwar ta ta zahiri ta samu hira da Kafar yada labarai ta Bbc hausa a cikin shirin su na daga bakin mai ita inda ta amsa tambayoyi bisa ga ‘adar shirin

Advertising

A cikin hirar Hauwa waraka ta bayyana takitaccen tarihinta da yadda aka yi ta shiga film da ma daina film din na tsawon sasu shekaru kana da dawowar da tayi a karo na biyu film din da ta fi so da dalilin da ya sa take fitowa a mara kunya da sauran su.

Hauwa ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda wasu ke munana mata zato a zahirin rayuwar ta inda ta bayyana tasan da mukullin wuta ahannun wasu mutanen yake baza su bawa dan film ba amma ta godewa Allah ta yadda da Annabawa da mala’iku da da kalmar shahada ta kuma san ita din wacece dan haka baya damunta.

Hauwa ta bayyana koda wani abu zata yi mara kyau da zarar ta tuna mutuwa takan ji duniyar ma ta fita a ranta haka zalika ta bayyana ta ji ta da yan kudi na biyan bukata ya fi komai sak ta farinciki dukdai a cikin birar da ma wasu tambayoyi da ta bada amsoshin su.

Advertising

Ga cikakiyar hira.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button