Labaran Kannywood
Wani dan kalo ya kasa hakuri ya rungume Safara’u a daidai lokacin da take wasan sallah.
Wata sabuwa jarumar masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Safara’u wanda ada take taka rawa acikin shirin Kwanacasa’in tayi wani wasan sallah a kasar Niger daya janyo cece kuce.
Kamar yadda mai karatu yasani yanzu Safara’u ta karkata fagen wake waken hausa ta bangaren Hausa hip hop, inda take rera wakar tata tareda mawaki Mr442 da ola of kano.
Sai dai bayan halartar wani babban taron wasan sallah wanda aka gudanar a kasar Niger wani masoyin Safara’u yakasa hakuri bayan da mawakiyar take kan rera waka inda yataso da gudu ya rungumeta cikin bainar jama’a abinda ya bawa kowa mamaki gadai Bidiyon a kasan.