Labarai
Allahu Akbar Yadda mata Da maza suka hau gyaran makabartar gidan Gona dake garin kano.
Yadda Al’umma Maza da Mata suka fita domin Gyaran Makabartar Gidan Gona a jiya ke nan.
Advertising
Sai dai har yanzu Makabartu a Jahar Kano na neman agaji daga al’umma kan yadda Ruwan sama ke haifar da Ruftawar Kabarurruka ga kuma rashin Kasa da isassun Kayan aikin da za a gyara.
Gyaran Makabartar da Kwamitin Kula da Makabartu na Jahar Kano bisa sanya Idanun Alh Yusuf Tukur Tarauni da kuma sashen kula da ayyuka na Karamar Hukumar Gwale bisa Jagorancin Hajiya Gambo Uwar Marayu sun nemi Jama’a da su kai dauki Makabartun Jahar nan domin tsomo su daga halin da suke ciki.
Masha Allah muna rokon allah ya kara basu juriya da hadinkai wajen kula da wannan makabar ta.
Advertising
Advertising