Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wasu Yan bindiga sukai garkuwa da Amarya da Ango a birnin Katsina

Wanni mumunan labari Yadda Yan bindiga sukai yi garkuwa da wasu sabbin ma’aurata bayan kashe jami’an duda biyu da sukai a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.

Advertising

Mazauna unguwar sun shaida, yan bindigar sun far mu su ne da misalin karfe 1:25 na dare, kuma sun shafe sa’a guda su na harbe-harbe ta ko wane bangare.

Sun kuma kara da cewa yan sa-kan sun rasa rayukansu ne a lokacin da suke kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu yan sa kan.

Rahotanni ya bayyana cewa ganin yan bindiga sunfi karfin su hakan yasa suka janye jikinsu.

Advertising

Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa yan bindigar sun shiga unguwar ne a kan babura jiya ɗauke da bindigogi suna harbe-harbe a kowane ban garen garin.

Mutumin yace yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata.

Ya kuma ce baya ga ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.

BBC ta rawaito cewa wannan ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.

Bugu-da-kari SP Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.

Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji Albdulkarim Faca -Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan mabovarsu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button