Advertising
Advertising
Labarai

Bidiyon da wani matashi yaje kabarin wata mata yana zaginta matashin ya shiga hannu yan sanda.

Kurnkus Yan sanda sun kama matashin da ya ringa surfawa wata mata zagi tana kwance a kabarinta.

Advertising

A safiyar lahadi ne aka wayi gari da wallafar wani faifan video da wani dan daudu ya wallafa yana kan kabarin wata mata yana zagin ta.

Sai dai kuma tuni Abdullahi Ƴar-dubu ya shiga hannun ƴan sandan Caji-ofis ɗin Sharada, inda yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama matashin, inda ya ce, tuni Mukaddashin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abubakar Zubairu ya bawa DPO na Sharada, SP Abdulrahim Adamu umarnin a kamo wannan matashi.

Advertising

Ya ƙara da cewa yanzu haka an kamoshi kuma an mikashi babbar shelkwatar rundunar yan sanda da ke bompai.

SP Kiyawa ya ce nan gaba kaɗan za a sanar wa da al’umma halin da a ke ciki.

Wannan shine Bidiyon da wannan matashi ya wallafa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button