Gaskiya ta bayyana: Rikici na kokarin Barkewa akan Wakar Asosa ta Ado Gwanja da Yawale na kwana Chasa’in.
Wakar Asosa “Chass” ta Ado Gwanja ashe itama satar fasaha yay kaman yadda yay a wakar “Warrr” kaman yadda muke samun labarin hakan.
Idan baku mantaba a kwanan baya da Ado Gwanja ya saki wakar “Warrr“, tana tsaka da tashe sai gashi an gano wakar Marigayi Maman Shata ce Gwanja yay mata gyare gyare.
In baku manta ba cikin wakar ta Warrr akwai zagi a cikin ta, Haka itama wakar marigayin maman Shata itama akwai zagi mai muni wanda bazamu iya rubuta muku shiba anan.
Haka bayan an gano wakar ta maman shatan Gwanja yayi wata wallafa a sharin sa inda yake cewa: Sun gano ni Sun gano ni.
To haka itama wannan wakar ta “Chass” Wadda ake ce mata lakabi da “Asosa” Itama mawakin ya saceta ne kaman yadda ya saci wakar Warrr.
Kuma a wannan karo Gwanja ba wakar maman shata ya sata ba face wakar Auwal Ishaq wato Yawale mai fitowa a kurma cikin fim din kwana chasa’in wanda arewa24 ke haskawa.
Jarumar data fallasa wannan abu itace ummi karama waddda take fitowa a shiri mai dogon zango na Labarina, Hausawa sukace magana a bakin mai ita tafi dadi.
Ga Bidiyon nata nan.