Advertising
Advertising
Labarai

Ta bayyana Shekara ya sake shekara daga jamhuriyar NNPP Zuwa PDP.

Atiku ya sauka a Kano domin karɓar Shekarau zuwa PDP

Advertising

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya isa Kano.

Atiku, wanda ya samu rakiyar abokin takararsa Gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, lyorchia Ayu ya tare shi, ya je Kano domin tarbar tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau zuwa jam’iyyar PDP.

Atiku ya bayyana zuwan sa ne a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yau Lahadi.

Advertising

Ya ce: “Na zo cibiyar kasuwanci ta jihar Kano Kwanaki masu zuwa za su zama na gwagwarmaya,” in ji Atiku.

Har Yanzu dai Ficewar Malan Ibrahim Shekarau bata fito ba amma magoya bayan sa sunce ya a gobe Litinin suke sa ran ficewar sa daga jamhuriyar NNPP.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button