Labaran Kannywood

Yadda aka tesa keyar dan daudun daya je yana zage zage a kabarin wata mata.

Wani Al’kali ya tesa keyar dan daudun daya je kabarin mahaifiyar abokinsa yana zage zage zuwa gidan maza domin ya girbi abin da ya suka.

Idan baku manta ba a sati biyu da suka gabata an ga wani Bidiyon wani dan daudu daya je yana zage zage kan kabarin wata baiwar Allah wadda yake cewa mahaifiyar abokin sa ce.

Tuni bayan wannan zagi da yay Hukumar yan Sanda jihar Kano tasa aka kamo matashi inda ba ai wata wata ba akai kaishi gaban kotu.

kotun Shari’ar Muslunci dake zaman ta a Gama PRP karamar hukumar nasarawa karkashin jagorancin mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad, Ya aike da matashin mai suna Abdullahi umar wanda ake kira da Yar Dubu kurkuku.

Inda ake cigaba da neman abokin cin mushen nasa wanda ya dauke shi Bidiyon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button