Labarai

Innalilahi wa’innailaihi raji’un Wani gini ya ya wado a kasuwar waya dake Berut dake Kano.

A na fargabar rasa rayuka bayan da gini ya rushe a kasuwar waya da ke kano a yammacin yau talata.

Wani gini mai hawa uku ya ruguje a wata shahararriyar kasuwar waya da ke Titin Beirut a jihar Kano a yau Talata.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a lokacin da ginin ya ruguje kan ‘yan kasuwa da masu sayar da abinci da sauran mutane a kasuwar.

A cewar shaidun gani da ido da suka zanta da wakilin Daily Nigerian Hausa, sun ce a halin yanzu mutane da dama sun maƙale a cikin ɓaraguzan ginin.

Wani shaidar gani da ido ya ce an fito mutane uku da ransu amma da yawa suna makale a cikin baraguzan ginin.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto.

ku cigaba da bibiyar mu dan samun inda labarin ya tsaya, Tun jiya da aka samu mamakon ruwan sama a garin na kano ake samun rugujewar gidajen kasa kawo washegari.

Muna rokon allah ya kare al’umma musulmi baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button