Advertising
Advertising
Labarai

Video Wata Uwa da ta siyar da jaririn ta akan kudi naira budu 600 Asirin ta ya tonu.

Hukumar ƴan sandan jihar Ogun ta kama matar mai shekaru 23 (an sakaya sunanta), wacce ake zargi da sayar da jaririnta mai kimanin sati uku da haihuwa akan farashin kudi N600,000.

Advertising

Mai magana da yawun bakin ƴan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, Ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta a ranar Alhamis.

Oyeyemi ya ce an kama matar ne a ranar 18 ga watan Agusta, Bayan ya kai kara matar tasa wajen yan sandan Mowe da ke Ogun.

Kakakin ya ce mahaifin jaririn ya ba da rahoton cewa yana soyayya da wacce ake zargin, sai ta samu juna biyu kuma ya kama mata hayar wani gida da take zaune har ta haifi yaron.

Advertising

Ya bayyana cewa wacce ake zargin ba zato ba tsammani tare da jaririn daga gidan makonni uku bayan haihuwa, sai aka neme ta a ka rasa, inda garin bincike, a ka gano ta a wani otal ta na sharholiyar ta da wani mutum.

“Duk kokarin da aka yi na sanin inda jaririn ya ke ya ci tira,” in ji Mista Oyeyemi.

Ya ce jami’in ‘yan sanda na reshen Mowe, SP Folake Afeniforo, ya yi cikakken bayani kan jami’an da suka gudanar da bincike a wurin kuma an kama wacce ake zargin.

Oyeyemi ya ce, da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta sayar da jaririn ne a kan Naira 600,000 ga wani a jihar Anambra.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa wadda ake zargin ta ce kawarta ce ta kai ta wajen mai saye kuma suka raba kudin daidai-wa-daida.

A cewar kakakin, an kama kawar kuma ta tabbatar da ikirarin matar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button