Advertising
Advertising
Labarai

Yanzu Yanzu Wani al’amari yafaru a garin Katsina na Cutar Kyandar Buri.

Yanzu Yanzu Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da cewa mutum hudu da suka kamu da cutar kyandar biririka, inda wasu kuma 53 suka kamu da cutar amai da gudawa ta kwalara a jihar.

Advertising

Daily Nigeria ta rawaito cewa, Kwamishinan lafiya na Jihar ta Katsina, Yakubu Danja, shi ya tabbatar da hakan a wani taro da aka shiryawa ma’aikatan lafiya a jihar.

Danja ya ce an gano sabbin mutane da suka kamu da cutar ne bayan gwaji da aka yi wa mutum 27 a baya-bayan nan.

A cewarsa, mutum tara cikin 27 din da ake zargi sun kamu da cutar sun fito daga wasu kananan hukumomi da ba a bayyana ba a jihar.

Advertising

An bukaci duk mazauna Garuruwan da Abubuwan Suka faru da su Zauna a wajajen.

Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar da suka bin dokokin lafiya sannan kar suyi kasa a gwuiwa wajen ziyartar cibiyar lafiya da ke kusa ko asibitoci idan suka fara ganin alamu da basu saba gani ba.

Ya ce babu dai wanda ya mutu cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar inda tuni aka yi wa wadanda suka kamu jinya tare kuma da sallamarsu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button