Ba Mu Kama Safara’u Da Mr 442 Ba Amma Har Yanzu Muna Nemansu Cewar Shugaban Hukumar Tace Finafinai Isma’il Afakallah
Mun samu wani bayani daga Indabawa Aliyu Imam Wanda ya tattauna da Sugaban hukumar tace fina finai Isma’il Afakallah
Na ziyarci hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano da ke unguwar Hotoro. Mun tattauna batutuwa da dama tare da shugaban hukumar Malam Isma’il Na’abba Afakallahu wanda mutumin kirki ne mai son kawo gyara. Mun yi batun yaran nan masu wakokin batsa wato Mr 442 da Safara’u Kwana Casa’in da kuma wakar wani Yaro mai suna Ado Gwanja ta a sosa baya chass.
Kafin Ado Gwanja ya saki wakar Chass Hukumar tace fina-finai ta tura masa da gayyata sai ya ce yana cikin uzuri sai ya sa kafa ya tafi Ghana ya saki wakar a can. Amma Afakallahu ya tabbatar min cewa ko ba dade ko ba jima dole Gwanja ya hallara a gaban hukuma ko kuma a dauki mataki mai tsauri a kansa.
Maganar kama yaran nan Mr 442 da Safara’au ba gaskiya ba ne, ba’a kama su ba, don ba sa ma Nijeriya. Amma dai Malam Afakallahu ya tabbatar min cewa sun jima suna farautar yaran amma sun ki zuwa Kano. Haka nan Shugaban hukumar ta tace fina-finai ya ba ni tabbaci cewa duk wani Otal da ake hasashen suna zuwa sai da hukumarsa ta bi su a Kano don a kama su, amma ba su zo saboda sun san idan suka zo Kano za a kama su kuma ba za su ji da dadi ba.
Shugaban Hukumar ya kara da cewa babu shakka komu dade ko mu jima sai Jaruman uku sun halatta a gaban sa, kuma sai sun nuna musu kuskuren su.