Innalilahi Wa’innailaihi Raji’un Wani Gini yayi Sanadiyar Halaka wannan yara guda biyu.
Wani Al’amari mai ban Tausayi Daya Samu Mahaifin Raran nan guda biyu, Shine Yadda wani gininakota ya danne su har lahira A ranar 28 ga watan daya gabata.
Wannan abu ya faru ne a garin kano a ranar da aka samu ambaliyar ruwa a wajaje da dama a unguwar mandawari dake kwaryar birni kano.
Wadannan yaran, ‘ya’yan mahaifiyar su ce ta haihu Amma jaririn yazo babu rai kaman yadda mahaifin Yaran ya fada mana, Ya kuma bayyana cewa da safe aka binne jairin data haifa, bayan an gama
Mahaifin Nasu ya koma asibiti wajen matar tasa saboda a asibiti ta haihu domin ci gaba da kula da ita. Sai akayi masa waya Suma wadannan Gini ya fado musu gaba daya sun mutu. Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.
Tuni akai jana’izar su kaman yadda addinin musulunci ya tanadar ‘Ya’ya uku a rana daya. Don Allah ku Saka shi cikin addu’a.