Advertising
Advertising
Labarai

Yadda waniatashi mai kimamin shekaru 18 ya rasa ransa yayin ceto saniyar sa a gogi.

Matashi Mai suna Adamu Musa dan kimanin shekaru 18 da yake zaune a unguwar magina a Cikin garin Buji a jihar Jigawa ya rasa ransa a dai dai lokacin da yake kokarin ceto saniyar sa data zame ta wada kogi.

Advertising

Kakakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar farar hula ta, NSCDC, reshen jihar Jigawa CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a 4 ga watan Satumba.

Ya ce lamarin ya faru ne a jiya Asabar, da misalin karfe 02:00 na rana, lokacin da matashin ya kaɗa shanunsa guda biyu zuwa gona, ya kuma bar su su yi kiwo a kusa.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin shanun sai ta zame ta faɗa cikin ruwan da ke kusa da gonar da su ke kiwon.

Advertising

PRO ɗin ya ƙara da cewa, a lokacin da saniyar ta faɗa, sai Adamu ya yi maza ga bita cikin ruwan domin ya ceto ta, amma sai ya nutse a ciki.

Shehu ya ce duk ƙoƙarin da mutanen yankin da jami’an NSCDC suka yi na ceto shi, ba a sami gawarsa ba sai karfe 01:00 na safiyar Lahadi.

“An kai gawar asibiti, inda a ka bincika ta sosai aka tabbatar da mutuwarsa, sannan aka mika wa iyayensa domin su yi musu jana’iza yadda ya kamata, inda ita kuma saniyar a ka ce to ta da ran ta,” in ji Shehu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button