Bayan yasamu karaya uku sakamakon gidan da yafado a kasuwar beirut yau Allah yayi masa Rasuwa.
Innalilahi Wa’innailaihi Raji’un Rayiwa kenan kowa ita yake jira, Bayan yasamu karaya uku sakamakon gidan da yafado a kasuwar beirut yau Allah yayi masa Rasuwa.
Kamamar Yadda duk mai bibiyar kafar sada zumunta ya san labarin wani dogon gini daya rushe a kasuwar beirut dake kano.
Wani gini mai hawa uku ya ruguje a wata shahararriyar kasuwar waya da ke Titin Beirut a jihar Kano a yau Talata.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a lokacin da ginin ya ruguje kan ‘yan kasuwa da masu sayar da abinci da sauran mutane a kasuwar.
A cewar shaidun gani da ido da suka zanta da wakilin Daily Nigerian Hausa, sun ce a halin yanzu mutane da dama sun maƙale a cikin ɓaraguzan ginin.
Wani shaidar gani da ido ya ce an fito mutane uku da ransu amma da yawa suna makale a cikin baraguzan ginin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto.
Ƙarin bayani na nan tafe…
Muna samun wannan rahoto Innalillahi wa inna ilaihi rajiun , Allah yayiwa dan uwa Danladi rasuwa yau , wanda yayi karaya ukku asanadiyya ibtila’e dayafaru a kasuwarmu ta beirut , zaayi jana’izarsa a Rimin Kebe Gidan Dakin layin Mal Kabiru. Damisalin karfe 3:pm