Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yanzu Yanzu Wata Sabuwar Sanarwa Ta Fita Daga Hukumar NBC Ta Nigeriya A Game Da Wakar Warr tlTa Ado Gwanja.

Hukumar kula da kafafen Sadarwa ta “NBC” a Najeriya ta haramta wakar Warr wadda sanannen mawakin masana’antar kannywoos “Ado Isa Gwanja” ya yi a baya-bayan nan.

Advertising

A sanarwar da NBC ta fitar tace, wakar “Warr” ta bayyana rashin tarbiyya da kalaman da basu dace ba a cikin ta.

Hukumar tace, a cikin wakar akwai zagi kai tsaye da kuma nuna yadda wasu ke tangadi bayan sun bugu da barasa ko kuma giya.

Baya ga kalaman da tace sun saba doka, NBC tace a hoton bidiyon wakar ta “Warr” wadda yanzu haka ta karade shafukan sada zumunta da kuma Youtube, an nuna yadda ake shan barasa kai tsaye.

Advertising

NBC ta ce hakan ya saɓa sashe na 3.18.2, da kuma na 3.9 na hukumar kula da kafafen sadarwa ta Najeriya.

Bugu da kari, NBC ta nuna damuwa kan yadda ake ta yada wakar a wasu gidajen talabijin na Arewacin Najeriya, wanda hakan yasa take tunanin cewa kafofin basu saurari wakar da kyau ba kafin su saka ta duniya ta gani.

Wakar “warr” da “Cass” da Ado Gwanja ya saki a baya-bayan nan na daga cikin wakokin da suka ja hankali sosai a tsakanin matasa a Arewacin Najeriya, musamman irin yadda suke kwaikwayon baitukansu a shafukansu na TikTok

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button